• Labaran yau


  Covid-19: Tarihi ba zai yafewa gwamnatin tarayya ba idan yan Najeriya sun kamu da yunwa - Tinubu

  Tsohon Gwamnan jihar Lagos Bola Ahmed Tinibu ya bukaci gwamnaytin tarayya ta kare yan Najeriya daga yunwa yayin da take tafiyar da harkar kariya ga wasu cutuka da coronavirus.
   
  Jigo a jam'iyar APC, Tinubu ya ce tarihi ba zai taba yafe wa gwamnatin tarayya ba idan yan Najeriya sun kamu da yunwa saboda cutar coronavirus.
   
  A wata sanarwa da ya fitar ranar 15 ga watan Aprilu, Tinubu ya ce tsarin fuskantar shawo kan cutar da aka dauka zai taimaka wa kananan yan kasuwa ne kawai, yayin da aka bar masu kananan sana'oi dav kananan albashi a baya.
   
  Ya yi kiran a fadada shirin ciyar da dalibai a makarantu, kuma a bayar datallafi.
   
   
  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Covid-19: Tarihi ba zai yafewa gwamnatin tarayya ba idan yan Najeriya sun kamu da yunwa - Tinubu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama