Rundunar yansandan jihar Kano ta tabbatar da kama Limamai goma sha biyar bisa zargin saba dokar hana zirga zzirga da cinkoson jama'a saboda dakile cutar coronavirus a jihar.
Limaman da aka kama sun jagoranci Sallar Juma'a ne, wanda hakan ya saba wa doka da Gwamna Ganduje ya sanya saboda ,matsalar cutar Covid-19. Wadanda aka kama Limaman Masallatan Juma'a ne a kananan hukumomin Birnin Kano watau Kano Municipal, Garko, Gwale, Karaye, da Tarauni.
Kakakin hukumar yansanda jihar Kano Abdullahi Haruna ya ce, jami'an hukumar Hisbah na jihar Kano ne suka kama Limaman, daga bisani suka mika su ga yansanda domin fuskantar tuhuma.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari