• Labaran yau


  Coronavirus: Dokar hana fita, mata sun yi zanga zangar rashin amincewa a jihar Delta

  Mata da dama sun gudanar da zanga zanga a garin Sapele na jihar Delta domin nuna  rashin amincewa da kara wa'adin dokar hana fita da mako biyu nan gaba a fadin jihar.

  Gwamna  Ifeanyi Okowa ya kara wa'adin mako biyu, bisa dokar hana fita dake aiki a fadin jihar kawo yanzu a wani jawabi da ya fitar ranar  14 ga watan Aprilu saboda cutar coronavirus.

  Matan sun yi korafin cewa basu da abin da za su ciyar da iyalinsu sakamakon dokar hana fita. Sun bukaci Gwamnatin jihar ta dage dokar hana walwala domin su fito su nemi abinci.

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Coronavirus: Dokar hana fita, mata sun yi zanga zangar rashin amincewa a jihar Delta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama