Rahotun BBC Hausa
Shugaban Amurka Donald Trump ya kira Shugaba Buhari na Najeriya a yau Talata domin tattaunawa kan yaki da annobar korona.
Mai
taimaka wa Shugaba Buhari a kan kafafen sada zumunta Tolu Ugunlesi ne
ya bayyana hakan, inda ya ce Trump ya yi alwashin tallafa wa Najeirya.
Annobar
na ci gaba da daidaita tattalin arzikin kasashen duniya, abin da ya sa
kasashe mataluta ke neman tallafi ruwa a jallo domin ganin bayan cutar.
Ko
a jiya Litinin sai da biloniyan dan kasuwar China Jack Ma ya aike wa da
Nahiyar Afirka tallafin kayan yaki da cutar da suka hada na'urar
ventilator 300 da takunkumin rufe fuska dubu 500 da kayan kare kai
2,000.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari