Type Here to Get Search Results !

Yadda uwargida ta kashe wata mata da 'danta ta bizinesu a gadinarta sakamakon kishi

Mahukunta sun damke wata uwargida da ta kashe wata mata da 'danta bayan ta zarge ta da yin kwartanci ga mijinta a gundumar Neno na yankin kudancin kasar Malawi.

Majiyar Mujallar isyaku.com ta tattaro cewa wannan uwargida tana zargin cewa wannan mata tana soyayya da mijinta, kuma ta kasa hakuri. Sakamakon haka ta gayyaci matar zuwa gidanta.

Bayan matar ta zo tare da wani 'danta 'dan karamin yaro, sai ta basu abin tabawa na cimaka, yayin da matar ta dukufa hankalinta ya koma ga abin motsa baki, sai uwargida ta zagaya ta dauko makami ta kwantar ma wannan mata a kai, kuma ta kasheta tare da danta.

Bayan uwargida ta aikata wannan mugun aiki, sai ta tone rami ta bizine wannan mata tare da 'danta a cikin gadenarta.

Daga bisani dai asiri ya tonu, kuma 'yansanda sun damke uwargida, kuma ta kaisu har wajen da ta kashe ta bizine wannan matar. 'Su dai 'yansanda, sun tone wanan gawa, kumasuna gudanar da bincike.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN