Type Here to Get Search Results !

Safeton 'dan sanda ya yi marisa ya kashe matarsa da bindiga



Rundunar yansandan jihar Bayelsa ta kama wani jami'in dan sanda mai suna
Tuddy Warebayigha, bayan ya harbi matarsa mai suna Charity da bindiga, sakamakon rikicin iyali dangane da yaya da suka haifa. Lamari da ya sa matar ta mutu.

Safeton dan sanda Tuddy Warebayigha, wanda ke aiki a caji ofis na yan sanda da ke garin Kaima a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma na jihar Bayelsa, ya bi matarsa ne zuwa hanyar gonarta, ya harbe ta a kafa, daga bisani ya harbe ta a ciki.

ISYAKU.COM ya samo cewa, safeton ya yi barazanar halaka duk wanda ya zo kusa da shi bayan ya harbi matarsa.

Rahotanni sun nuna cewa Safeto Tuddy dan barasa ne na gaske, kuma ya sha yin barazanar cewa zai koya wa matarsa hankali kamar yadda wani ganau ba jiyau ba ya fada wa Jaridar The Nation.

Kakakin hukumar yansandan jihar Bayelsa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama Safeto Tuddy, kuma yana fuskantar bincike a sashen CIID na rundunar.


DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN