Yadda fasinja ya sace wa direban mota wayar salula da N20,000

Rahotun Legit Hausa

An gurfanar da wani fasinja dan shekara 27, Tolu Omini-Ekpo a ranar Talata a gaban kotun Majistare da ke Tinubu a Legas kan zarginsa da sace wa direban tasi wayar salula da kudinta ya kai N76,000 da kuma N20,000 kudin mota.

 'Yan sanda sun tuhumar Omini-Ekpo da laifin sata. Amma bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba. Mai shigar da kara, Sufeta Ajaga Agboko ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin a ranar 9 ga watan Maris misalin karfe 2 na rana a Eko Hotel and Suite da ke titin Adetukumbo Ademola a Victoria Island a Legas.

Ya yi ikirarin cewa wanda aka yi karar ya sace waya kirar Tecno da kudinta ya kai N76,000 da kuma N20,000 mallakar direban tasi din Mustapha Adebayo. Mista Agboko ya yi ikirarin cewa wanda akayi karar ya tambayi direban ya bashi aron wayarsa domin ya yi amfani da manhajar lissafi daga nan kuma ya tsere bayan an tsaya inda zai sauka.

Mista Agboko ya kuma kara da cewa wanda aka yi karar ya kuma sace wata Infinix da kudinta ya kai N46,000 mallakar wani Mista Moses Okedeji. Mista Agboko ya ce laifin ya sabawa dokokin jihar Legas sashi na 287 na shekarar 2015. Shugaban kotun, Majistare T.A. Anjorin-Ajose ya bayar da belin wanda aka yi karan kan kudi N20,000 tare da mutane biyu da za su karbi belinsa.

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN