Ko wa jima ko wa dade za a gan talaucin da ya faru a Najeriya | ISYAKU.COM


Rahotun Leadreship Hausa

Talauci na daya daga cikin matsalolin da wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta haifar a Nijeriya da nufin kowa ya tashi a tsaye ya rike kansa idan zai iya ko ba zai iyaba. Lamarin da mutane masoya wannan gwamnati ke ganin kamar wani abin alfahari ne a ce kowa ya koma gona ko kuma ya koma kan bola tattara kayan shara domin neman abinci daga cikin bolar, yadda idan an rasa kayan bola matasa ke wucewa satar kayan wanda su ka yi sake.

Kasashen da ke irin wannan tsari kamar su Jamus ko Indiya ko China da makamantan su, kasashene da suka ginu a kan wannan hanya kuma su na da masana’antu da bayar da tallafi kan kiwon lafiya da ilmi da samar da abinci da sauran kayan more rayuwa na yau da kullum har da inshore da alawus ga marasa aikin yi. Sabanin a Nijeriya da idan mutum ya shiga wahala musamman a wannan lokaci sai ko ya nemi rayuwa ko da tsiya ko da arziki, saboda rashin abin yi da kuma rashin tallafi musamman a wannan lokaci ba kamar yadda a ka saba a gwamnatocin baya inda ake agazawa a fannoni da daman a rayuwa ba. Duk da irin wahalar da ake sha a kasar nan kashi 60 cikin dari na talakan wanda ke shan wahala idan ka ce masa gwamnatin Buhari ta gaza wani yanzu zai ci mutuncin ka.

Yadda hatta wannan rubutu da na ke yi idan na biye irin wadannan mutane da tuni na daina. Amma kasancewar masu bugo waya su gode su nuna jin dadi sun fi yawa, kuma da dama sun fahimci gaskiya muke fada, shi yasa nake ci gaba da wannan rubutu duk da irin cin zarafin tura sakonni da wasu ke yi. Amma wasu idan sun kira waya sai su ce munyarda gaskiya kake fada amma ba laifin Buhari ba ne na wanda suka gabace shine don haka zai gyara idan ya dawo na kasan sa ke zagon kasa basa son sa basa son kasar. Hakan ya sa wasu ke yin kirari da cewa Buhari Annabin wawaye, ko raba talaka da Buhari sai Allah.

Mun ji mun yarda amma kowa ya rubuta ya ajiye akwai lokacin da zai zo dole yadda talaka ya ji a jikinsa haka suma shugabannin za su ji a jikin su, domin idan manya masu hankali sun ci gaba da nuna soyayya da samina wa adana wa Buhari, matasa a karshe talauci zai sa su bijiriwa gwamnati sai yadda Allah yasa hali ya kasance.

Saboda kasa kamar gidane idan mutum bai yarda ba ya daina kai cefane gidansa ya ce iyalensa kowa ya tashi ya dogara da kansa na tsawon wata guda, yaga yadda za su lalace, ban zaci za a kai wata guda ba za a samu karuwai da barayi a cikin gidan kamar yadda ke faruwa yanzu a Nijeriya yadda a nan gaba za a sha wahala kafin a gyara tunanin matasa da ‘yan matan da su ka zama barayi ko ‘yan shaye shaye ko sara suka, daga nan za a fahimci ashe Allah ya rufawa mutane asiri Buhari yazo ya kuntata ya tona musu asiri. 


Saboda a kullum haifar yara ake yi kuma kashe kudi ake yi a kansu wajen yin karatu amma babu wani shiri na gaskiya domin basu aikin daya dace da ilmin su sai N-power wanda har zuwa wannan lokaci ban yi zaton an dauki mutane dubu dari a wannan shiri ba. Kuma me ake zato yaro ya yi karatu ka ba shi da aiki shekara biyu kana bashi dubu talatin ya yi aure ya fara tara iyali ka katse kace ya tafi ya nemi abin yi, wanda na san shi lokacin da ya yi nasa karatun yana gamawa ga aiki wani lokaci har da abin hawa.


Daga nan sai gaba da zagon kasa tsakanin matashi da gwamnati su kullu. Kuma abin takaici wannan yaudarar duk a na yi wa masu karatune, jahilai da ba su samu karatu ba ba wani tanadi da a ke yi mu su sai basu kayan maye su bi ‘yan siyasa wanda daga bisani idan su ka samu mugaye su ka ba su makami za su aikata komai kamar yadda ke faruwa a wasu jihohi.

Hakan daga bisani zai kasance idan su na tsoron jami’an tsaro za su daina idan wahala ta yi wahala kuma sai kurum su zaman ‘yan tawaye sai neman wargaza kasa ta kowane hali, da fatar Allah ya kiyaye ya kawo mana karshen wannan lamari yasa shugabannin su hankalta su koma hanyar gaskiya. Bayan haka akwai matsaloli irin na lalacewar tarbiyya da neman abinci ta kowace hanya halas ko haram, ga barazana ta rashin tabbas yadda kowa idan ya wayi gari bai san me gobe za ta haifar ba, musamman yadda a wasu lokuta wanda ke ci ya ciyar da wani yanzu an wayi gari cikin kasa da shekaru hudu wanda ke taimakon wasu da abinci da kayan bukata yanzu an wayi gari shi ne ke neman taimako.

Saboda ya tara iyali, amma yanayin da a ka shiga ya sa abin hannun sa ya kare ba yadda zai yi saboda idan zai aura ko zai auras ko zai yi jinya ko wata hidima mai cin kudi sai ya sayar da kadara har an kai wani matsayi da yanzu babu kadarar da zai sayar ya koma maula ko bara. Yadda a masallaci daya idan an idar da sallah sai mutum goma ko fiye su tashi suna bara kowa na fadar matsalarsa babu mai jin ta wani saboda tsabar damuwa da talauci da suka dabaibaye mutane.

Mazauna karkara kuma kullum tura yaransu suke yi birane aikin wahala ko almajiranci don neman abin sawa a baka, har ya zamo iyaye kamara yaran sun dame su basu ki sun mutu ba ko sun bar inda suke don su huta da dawainiyar su. Maza sun lalace sun zama sai shaye shaye da ta’adda wasu ‘yan mata sun zamo karuwai kai har matan aure sun lalace. Tun masallatai na hana bara har sun kai ga mai ganin laifin wanda ke bara shima an wayi gari talauci ya addabe shi ji yake yi kamar ya yi barar, illa iyaka idan kana da masu tallafa ma daga yara ko makusanta shikenan za ka samu saukin lamarin.

Wani abin mamaki ya faru a wata unguwa yadda wani mai hali abin ya hannu ya kare, duk wata hanya da ya ke nema ta rufe. Aka wayi gari ba abin da za a ci a gidansa Allah ya jarrabe shi yaga babu yadda zai yi, bayan an yi sallah a masallacin unguwa ya tashi ya fadawa mutane halin da ake ciki ga yara yau kwanaki ba wanda ya ci ya koshi, sai ya fashe da kuka haka mutane su ka ta tallafawa su ma wasu na kuka.

Daga nan akwai wani malami ya kira shi gidansa ya auna masa mudu biyar na gari mudu biyar na shinkafa ya bashi naira dubu biyu yana karba sai ya fashe da kuka yace yau ni da ke bayarwa ni ne na koma mabaraci sai ya fadi har asibiti tsabar takaici, duk wanda ke ganin ba haka ba yazo zan kai shi har inda abin ya faru. A cikin kasuwar wunti da ke Bauchi akwai limamin wani masallaci da ya dinga wa’azi da yiwa Buhari kamfen a 2015 har aka rika tsanar sa, amma sai aka wayi gari a bara jarinsa ya karye babu abin da yake yi sai a zo kasuwa a zauna a tashi hannu wofi.

Masallaci kuma ba abin da ake samu sai ko ya bada sallah kowa ya tafi, aka wayi gari ya shiga damuwa wata rana an tayar masa ikama ya tsaya zai ja sallah sai jiri ya kwashe shi aka kama shi aka zaunar aka masa fifita ya dawo hayyacin sa, ya ce wallahi kwana uku kenan baici abinci ya koshi ba, don bai san yaya ma ta ke yi da yara ba idan yayi asuba ya fito kasuwa sai bayan isha yake komawa. Nan a ka nemi taimako aka tara dubu ashirin da bakwai a ka saya masa buhun shinkafa aka bashi sauran canjin.

Wallahi a nan Bauchi akwai matar da taje kasuwar Central ta sayi shinkaf tara da yarinyarta yayayya sai ta duba jaka kamar da kudi daga karshe ta ce tabar kayan da ta saya a wani shago yarinya ta jirata a wajen tana zuwa ta tafi da shinkafar ashe gida ta wuce.

Mutum ya jira har ya gaji sai suka sa yarinya a gaba har gida suka yi sallama da ta leko taga yarinya da mutane tace su shiga, sai ta nuna musu shinkafa a kan wuta ga yara gewaye da murhu suna jira tace wallahi ba yadda za ta yi yau kwanaki ta rasa me za taba yaran sun dameta da kuka duk masu taimaka mata sun gaji mijinsu ya gudu ya barsu don haka dole tasa ta daukar wannan matsaya, haka ‘yan kasuwa suka tausaya su ka ba ta yarinyarta suka tafi suka barta. Irin wannan misali idan zan bayar dasu a cikin Bauchi kurum zan bada masu yawa game da kuncin rayuwa abin da ke jefa mutane cikin matsala.

A takaice akwai labarin da na karanta a kudancin kasar nan kwanaki an kama gungun ‘yan fashi da makami yawancin su sun yi karatu kusan kowa yana da takardar digiri yayi NYSC ba abin yi. Akwai wanda yace ya nemi aiki sama da sau dari ya je jarrabawar daukar aiki yafi sau talatin bai samu aiki ba. Nan take aka ce kwamishinan ‘yan sandan yasa aka rika tafiya dasu daya bayan daya gidajensu kowa yana dauko takardar karatunsa, haka ya hallara su ya tafi ya kaisu gaban gwamna daga nan aka fara neman yadda za a taimaka, wannan wace irin kasa ce don Allah. Allah ya taimaka mana ya hada mu da masu tausayi masu kaunar mu ba sai wani makon.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN