An dakatar da bukukuwan al'adun kasar Masarautar Zuru da ake kora Uhola na shekarar 2020 har illa masha Allahu.
Mai Martaba Sarkin Zuru Alhaji Muhammad Sani Sami Gomo na 2 ne ya sanar da haka yayin zantawa da manbobin kwamitin tsare-tsare na bukukuwan Uhola a fadarsa ranar Litinin.
Abba Muhammed Zuru ya ruwaito cewa, Sarkin ya ce " Bisa la'akari da matsalar annobar cutar Coronavirus COVID 19, zai yi matukar wuya a iya gudanar da wannan buki a cikin wannan yanayi."
Sakamakon haka Sarkin ya bukaci manbobin kwamitin tsare-tsaren bukin Uhola su kasance cikin shirin ko ta kwana, amma ya sanar da dage bukin har zuwa badi.
Rahotun Isyaku Garba Zuru
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari