Gwamnan jahar Borno ya nemi agajin tsofaffin jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci

Rahotun Legit Hausa

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya gayyaci tsofaffin jami’an hukumomin tsaro da suka hada da manyan Janarorin Soja da manyan jami’an Yansanda zuwa wani muhimmin taro don duba yiwuwar taimakawa a yaki da ta’addanci. Gwamnan ya mika wannan gayyata hatta ga tsofaffin jami’an hukumomin tsaron sirri watau DSS, da sauran jami’an hukumomin tsaro domin su baiwa gwamnatinsa shawarwarin da suka kamata don shawo kan matsalar.

Zulum ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Maris a lokacin da ya gana da jami’an gwamnatin tarayya yan asalin jahar Borno dake aiki a hukumomi daban daban a babban birnin tarayya Abuja. Gwamnan ya yi wannan kira ne biyo bayan bukatar yin haka da wani tsohon babban Sojan mai mukamin Birgediya Janar ya yi, inda yace ya sadaukar da kansa domin baiwa gwamnati dabaru da salon yaki da zai taimaka wajen yaki da Boko Haram

 “Taruwanmu a nan duk saboda abu daya ne, domin gina jaharmu, kakanninmu ma sun yi irin wannan wajen farfado da kasar Borno a baya bayan mawuyacin halin da ta taba shiga a zamanin da, sun yi yake yake don gina al’ummomi. “Akwai bukatar mu zama tsintsiya madaurinki daya, mu manya da 2023 mu hade kai da don jahar Borno, ya kamata mu duba hanyoyin da zamu iya taimaka ma jahar Borno ta hanyar sake tsugunnar da yan uwanmu, iliminsu, kiwon lafiya, samar da ayyuka da tattalin arzikin Najeriya.

” Inji shi. A wani labari kuma, akalla dakarun rundunar Sojojin Najeriya guda 6 ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon wani mummunan harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suma kaddamar a ranar Lahadi a jahar Borno. Mayakan ta’addancin sun kai ma Sojojin harin ne yayin da suka bude ma ayarin motocin Sojojin wuta a kusa da kauyen Mayanti dake kusa da iyakar Najeriya da kasar Kamaru, yankin da yan ta’adda suka mamaye. “Mun yi asarar Sojoji guda 6 a wannan harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai mana.” Kamar yadda wani jami’in rundunar Soja ya tabbatar.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN