Abinda yasa aka tsige Sarki Sanusi - Tanko Yakasai

Rahotun Legit Hausa
Alhaji Tanko Yakasai, dan siyasa a arewa kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro Arewa Consultative Forum, ya bayyana dalilin da ya jawo tsige rawanin tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido a ranar 9 ga watan Maris din 2020.
A wata tattaunawa da aka yi da shi da jaridar Punch a ranar Lahadi, Yakasai ya ce dalilin farko da yasa aka tsige rawanin sarkin shine yadda ya ke wa wanda ya nada shi sarki biyayya, wato tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Wanda tuni kuwa suke da tsananin rashin jituwa da Gwamnan yanzu, Abdullahi Umar Ganduje.
Abu na biyu kuwa da ya jawo tuge rawanin tsohon sarkin shine rashin fahimtar tsohuwar al'adar jihar Kano wanda hakan yasa yake aiki ba tare da dubanta ba.
"An haifeni a Kano kuma na san al'adun masarautar. Tun da nake yaro har zuwa yau, da sarki mai ilimi da mara ilimi basu magana da yawa. Suna mutunta kalamansu. An haifa Sanusi a Kano ne amma tashin Legas ne da Kaduna. Mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne wanda ya kai matsayin babban sakata
"Al'adar ma'aikatan gwamnati ne balle wadanda ke aiiki a ma'aikatar lamurran kasashen waje na rashin zama a waje daya. Sarkin da farko yana rayuwa ne tare da tsohon ministan tsaro, Alhaji Inuwa Wada amma da mahaifinsa ya dawo sai suka canza shi.
"Sarkin asalinsa dan Kano ne amma bai rayu da jama'ar Kano ba har sai da ya hau karagar mulkin masarautar. Wannan ne tushen matsalar." Yakasai ya sanar da Punch.
Alhaji Yakasai ya kara da cewa, babban dan marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ne yafi cancanta da karagar mulkin amma kuma gwamnan lokacin sai ya dora Sanusi.
Kamar yadda ya ce, wani abu da ya kara tunzura gwamnan shine yawan maganar sarkin a kan komai kuma duk ra'ayoyinsa sun ci karo da ra'ayin al'adun jihar Kano din.
Wannan kuwa kamar yadda ya sanar, ya biyo baya ne saboda sarkin bai tashi a cikin Kano din ba.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN