• Labaran yau


  Duba jerin kasashen duniya guda goma da jama'a suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

  Rahotun Legit Hausa

  A yayin da duniya ta rike ta kuma dimauce akan cuta mai kisa da ta addabi kowacce kasa ta duniya wato Coronavirus, zai zama kamar ba yanzu ne ya kamata a bayyana kasashen da suka fi farin ciki a duniya ba Amma dai duniya ta fitar da rahoton kasashen da suka fi farin ciki a duniya a shekarar 2019, inda ta bayyana kasar Finland a matsayin ta farko a bangaren farin ciki da jin dadin rayuwa.

  Haka kuma rahoton yana duba kasashe akan abubuwa guda shida da suka hada da tattalin arziki, jin dadin rayuwa, harkar lafiya, walwala, kirki da mutunci tsakanin al'umma, rashin cin hanci da rashawa. A yadda rahoton ya bayar kasar da tafi kowacce ita ce kasar Finland, wacce take a yankin Turai. Sannan sauran kasashe biyar na cikin jerin duka daga yankin Turai ne.

  Daga kasar Finland sai kasar Denmark, Norway, Iceland da kuma kasar Netherlands. Najeriya da take da yawan mutane sama da miliyan 200 ta zama kasa ta 85 a duniya. Kasar Sudan ta Kudu ita ce kasar da ta zo ta karshe a duniya, kasar ta zama mutanen cikinta basa jimawa a duniya, bata da karfin tattalin arziki.

  Kamar yadda rahoton ya bayar na shekarar 2019, ga jerin kasashen guda goma a kasa:

  1. Finland
  2. Denmark
  3. Norway
  4. Iceland
  5. Netherlands
  6. Switzerland
  7. Sweden
  8. New Zealand
  9. Canada
  10. Austria

  DAGA ISYAKU.COM
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

  Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

  Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Duba jerin kasashen duniya guda goma da jama'a suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama