Allah
ya tona asirin wani safeton 'dansanda bayan wani dan fashi da makami ya
yi masa tonon siriri a ofishin 'yansanda sashen IRT da ke GRA Ikeja a
birnin Lagos. Shi dai wannan dan fashi ya ce safeto Asom Ubi ne shugaban
kungiyarsu ta fashi da makami, duk da cewa safeto Ubi jami'in 'dansanda
ne na SARS da ya kamata su kama 'yan fashi da makami.
Wannan
'dan fashin ya shaida wa jami'an 'yan sanda na IRT cewa kungiyarsu ce
karkashin jagorancin Safeto Ubi suka yi fashin wata motar kaya da aka
kiyasta kudin kayan a kan Naira Miliyan 145 a birnin Lagos. Safeto Ubi
ya jagoranci yan fashin suka tsayar da motar tare da yaron mota suka
daure su suka saka su a cikin boot na wata mota , daga bisani suka kai
su babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan, sai suka yar da su a gefen hanya
suka tafi.
New Telegraph ta ruwaito cewa safeto Ubi
tare da 'yan kungiyarsa sun sayar da kayakin da motar ta dauko a kan
Naira Miliyan 45, marmakin Naira Miliyan 145 a kasuwar Alaba, daga
bisani kuma suka sayar da motar.
Rigima ya kaure ne
bayan safeto Ubi ya ba dan fashin Naira 150.000, sakamakon haka dan
fashin ya tunkari safeto Ubi, wanda ya ce masa wai ba'a gama sayar da
kayakin ba. Amma bayan dan fashin ya tuntubi sauran 'yan kungiyarsu ta
fshi da makami na mutum 7 karkashin jagorancin safeto Ubi, sai ya gano
cewa ashe kason kudinsa a wannan harkalla Naira Miliyan 3 ne, amma
safeto Ubi ya bashi Naira 150.000.
Bayan wannan dan
fashin ya yi duk abin da zai iya yi domin safeto Ubi ya bashi ragowar
kudinsa amma ya ki, sai ya nufi ofishin 'yansanda na IRT marmakin SARS
inda safeto Ubi ke aiki, sai ya fasa kwai. Sakamakon haka, manyan
jami'an 'yansanda karkashin jagorancin CSP Phillips na sashen IRT suka
shiga bincike, har suka gano direba da yaron motar da aka karbe motar a
hannunsu, kuma aka kama safeto Ubi wanda ya tabbatar da laifinsa yayin
gudanar da bincike.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya
Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari