Ban san yaushe Muhammadu Sanusi II zai bar Loko ba – Sarki Abubakar Sabo

Rahotun Legit Hausa
Jaridar VOA Hausa ta yi hira da Mai martaba Sarkin Garin Loko, Alhaji Abubakar Ahmad Sabo, domin jin ta bakinsa game da dawo da Muhammadu Sanusi II cikin kasarsa.
Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya nuna cewa ya ji wani iri a ransa a lokacin da ya ji labarin tsohon Sarkin Birnin Kano Muhammadu Sanusi II zai yi zaman gudun hijira a Loko.
Sai dai duk da haka Mai martaban ya bayyana cewa ya zama dole a rungumi kaddarar Ubangiji game da wannan jarrabawa da ta fadawa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Garin Loko Abubakar Ahmad Sabo ya shaidawa ‘Yar jarida cewa Garin Loko ya yi wa mutumi irin tsohon Sarkin KanoMalam Muhammadu Sanusi II Kauye da yawa.
Mai Martaba Ahmad Sabo ya yi wannan magana ne a Ranar Litinin, 9 ga Watan Maris, cikin dare. A daidai wannan lokaci Muhammadu Sanusi II ya kamo hanyar zuwa Garin.
Idan ba ku manta ba, jirgin sama ya dauko tsohon Sarkin Birnin Kano ne daga Mahaifarsa zuwa Abuja. Daga nan kuma aka shirya motoci su dauko sa su ajiye a wannan Kauye.
Ban san yaushe Muhammadu Sanusi II zai bar Loko ba – Sarki Abubakar Sabo
Sarkin Loko Abubakar Sabo ya tausaya Muhammadu Sanusi II
Sarkin Loko ya na ganin cewa Muhammadu Sanusi II ba zai dade a wannan wuri ba kafin gwamnati ta canza masa wurin zama. Sai dai bai san yaushe ne za ayi hakan ba.
Game da lokacin da Sanusi zai bar Loko, Sarkin ya ce:
“A’a ya rage na gwamnati ne kuma wannan. Tun da abin ya faru, kin san dole a raba shi da wurin (fadar Kano). Amma ba zai cigaba da zama a nan (Loko) na din-din-din ba."
“Bai kamata ace irin wannan ya zauna a nan ba. Akwai wanda bai kai sa ba kamar Sarkin Gwandu, lokacin da aka ciresa, an kawo sa Garin Obi jihar Nasarawa”
Sarkin na Loko ya ce bayan wani lokaci gwamnati ta dauke Jokolo, ta maida shi Garin Kaduna. Don haka ya ke ganin ba za a iya ajiye Sanusi II a wannan Gari ya dade ba.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN