Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda

Rahotun Legit Hausa
Alhaji Umar Dikko ba mabaraci bane kamar mabaratan da ake gani a kan tituna wadanda ke neman sadaka daga hannun masu tausaya musu.
Alhaji Umar Dikko dai mabaraci ne amma yana da babban banbanci da sauran mabarata. Shi ne sarkin Maroka na yankin Ajegunle da ke jihar Legas, amma kuma ya kafa tarihin zama mabaracin da ya fi kowanne arziki a Najeriya.
Duk da yana da nakasa, Alhaji Umar na da tarin dukiya kuma yana da mata hudu ne da yara 18. Yana kasuwancin sufuri ne kuma ya mallaki kamfanin yin ruwan leda. Yana da gidaje ginannu guda biyar a jihar Kano.
A yayin da yake labarta yadda ya nakasa, Alhaji Umar Dikko ya ce, hakan ta faru da shi ne tun yana da shekaru uku kacal a duniya. Ya saba yawo a titunan don samun abinda zai ciyar da kan shi don iyayen shi sun sake shi.
“Na rasa kafa ne lokacin da nake da shekaru uku sakamakon cutar polio. Iyayena da sauran ‘yan uwana basu damu da ni ba balle su kula dani. Mahaifiyata ce take kokari kuma tana da yara bakwai. A lokacin da na kai shekaru 6, na fara kula da kaina saboda bana samun kular. Daya daga cikin ‘yan uwana ke kaini kasuwa in yi bara amma kudin muna kaiwa mahaifiyarmu ce wacce take kula damu.
Sarkin maroka: Mabaracin da ya mallaki gidaje biyar, motoci 20 da kamfanin ruwan leda
“A lokacin da na kai shekaru 15, na yanke shawarar dawowa jihar Legas. Bayan isowata ne na hadu da mabarata hausawa da ke Agege kuma tare muke fita bara. Amma akwai wanda ke bamu wajen kwana, wanda shi ke kwace duk kudin da muka samu sannan ya bamu na abinci kawai.
“ Bayan shekaru uku da na dauka tare da shi, na koma Ajegunle inda na hadu da wani dan garinmu. Shi yake turani amma ina bashi wani kashi na kudin da muka samu. Daga nan ne na fara tara kudina har na siya mota kirar bas wacce na bada ana min haya.
“Daga nan na kara siyan wata motar wanda daga haka ne na fara kasuwancin sufuri. Ina da motoci sama da 20 wadanda ke yawo daga Legas, Kano, Abuja, Kaduna, Jos da sauran jihohin arewa.”
Dikko ya bayyana cewa daga nan ne ya tafi gida Kano inda ya gina gida kuma ya zuba ‘yan haya a ciki. Amma kuma bai dena bara ba don ganin hakan yake kamar kasuwanci.
Daga nan ya kara gina wasu gidajen hudu inda ya bada hayar biyu tare da saka matansa hudu da yaransa 18 a ciki. Kamar yadda yace, ya yi aikin haji har sau uku kuma yana kula da iyalansa yadda ya dace.
“A shekaru biyar da suka gabata ne aka nada ni sarkin marokan Ajegunle kuma ina lura da lamurran bara da sasanci a tsakanin mabaratan. Amma ni yanzu na daina bara.” ya ce.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN