Sa’o’i bayan tube Sarki Sanusi II, aka nada Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado Bayero .
Muhimmman abubuwa game da Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero:
- Aminu Ado Bayero ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.
- Shi ne aka fara zaba a matsayin Hakimin Nasarawa, kuma mukamin Danmajen Kano wanda mahaifin shi Sarki Ado ya nada.
- Ya rike mukamai a Masarautar Kano da suka hada da: Turakin Kano da Dan Buran da Sarkin Dawakin Tsakar Gida da kuma Wamban Kano.
- Shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.
- Shi ne da na biyu babba a maza ga marigayi Sarki Ado Bayero.
- Ya yi karatun digirinsa a bangaren aikin jarida a jami’ar Bayero ta Kano.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari