Yadda wani ango ya sha dukan tsiya a ranar aurensa, karanta dalili

Rahotun BBC Hausa

An kori wani ango daga wajen bikinsa bayan matarsa ta farko ta je wajen domin sanar da amaryar cewa yana da mata biyu.

Asif Rafiq Siddiqi, wanda ke a tsakanin 34 zuwa 37, ya sha duka da mari daga wajen mahalarta bikin amaryar da zai kara aura.

An yaga masa kaya inda ya ranta ana kare ya samu wasu suka cece shi.
An dai halatta auren mata hudu a Paistan.

To sai dai kuma, duk da an halatta wa mutum ya auri mata hudu, to dole ne ya shaida wa sauran matansa kafin auren.

To sai dai ga dukkan alamu, Mr Siddiqi bai bi wannan tsari ba, shi yasa a lokacin da amaryar tasa ta samu labari, ita da 'yan uwanta ba su yi wata-wata ba suka lakada masa duka. Wannan lamari dai ya faru ne birnin Karachi.

Matar Mr Siddiqi ta fari mai suna Madiha Siddiqi, ta je wajen bikin ne tare da dansa, ko da ta isa wajen ta shaida wa masu bikin cewa: "Mijina ne, kuma shi ne mahaifin wannan yaron, ya shaida mini cewa zai je Hyderabad ne ya yi kwana uku".

Daga nan ne sai 'yan uwan amarya suka kai matar Mr Siddiqi wani daki ta huta, suka kuma nemi labarin komai ta kuma shaida musu.

Madiha Siddiqi, ta ci gaba da cewa, na auri Mr Siddiqi ne tun a shekarar 2016, lokacin ina karatun jami'a a Urdu da ke Karachi.

Ta ce "Bayan mun yi aure, ya je ya sake aure a boye ba tare da ya sanar da ni ba a shekarar 2018".
Mrs Siddiqi, ta ce da farko ya musanta cewa ya sake aure, amma daga baya sai ya amince cewa ya auri mata ta biyu.

Ta ce, matarsa ta biyu ce ta shaida mini cewa zai kara auren ta uku inda ta sanar da ita inda ake auren.
To daga nan ne sai 'yan uwan amarya suka fusata nan da nan suka fara dukansa tare da yaga masa kay
Jami'an 'yan sanda ne suka ceci Mr Siddiqi inda suka kai shi ofishinsu, to amma duk da haka sai da 'yan uwan amaryar suka bi shi suka jira shi a kofar ofishin suna jiran fitowarsa.

Da jami'an tsaron suka fuskanci haka, sai suka dauko Mr Siddiqi suka fito da shi suka sanya shi a wata mota kirar bas.

Can sai 'yan uwan amarya suka rinka barazana suna cewa, ka fito ko kuma mu cinna wa motar wuta.
A haka dai har 'yan sanda suka tafi da shi.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN