Wani Alfa ya shiga uku bayan ya dandana abin da ba huruminsa ba, duba abin da ya faru
February 15, 2020
Yan sanda a jihar Osun, sun gurfanar da wani Malamin addinin Musulunci mai suna Habeebulah AbdulRahma,n wanda aka fi sani da suna El-Edewy, a gaban Kotu a karo na biyu bisa zargin yi wa yar shekara 16 fyade a 2019.
Duk da yake iyayen yarinyar sun nemi a sasanta lamarin ba a cikin Kotu ba, amma saboda matsi daga kungiyoyi da kafafen yada labarai, sai yan sanda suka sake gurfanar da Habeebullah a gaban Kotu.
An tuhumi Habeebullah ranar Laraba 12 ga watan Fabrairu, da daukan yarinyar, ya kaita wani waje inda ya sadu da ita, da kuma shafar sassa na jikinta.
An bayar da belin sa har zuwa ranar da Kotu za ta sake zamanta.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari