Tap di jan: Wani mutum ya manne al'aurar matarshi da supa glu, karanta dalili

Wani mutum mai suna Denis Mumo dan shekara 36 ya manne al'aurara matarshi da supa glu bayan ya sami labarin cewa matarshi tana harka da maza lokacin da ya yi tafiya.

Denis, wanda ke yawan tafiya zuwa kasar Rwanda domin gudanar da sana'a, ya ba mutanen garinsu mai suna Kitui mamaki a kasar Kenya, yadda ya zuba supa glu a al'aurar matarshi kafin ya yi tafiya, sakamakon haka matar ta nemi agaji bayan ta fara jin matsanancin ciwo sakamakon raradin mannewan glu da mijinta ya lafta a al'aurarta.

An garzaya zuwa Asibiti da matar, yayin da Likitoci suka yi mamaki irin wannan hukunci da Mumo ya aiwatar wa matarshi, wanda hakan ya haifar mata da matsaloli na lafiya.

Bayan yansanda sun kama Mumo, ya shaida masu cewa ya aikata laifin ne bayan ya karanta sakonnin wayar matarsa, kuma ya gano cewa tana harka da maza har guda 4 idan baya gari.
 
Ya kuma nuna wa yansanda hoton tsiraicinta da ta aika wa daya daga cikin mutane da take lalata da su ida baya gari, inda ta rubuta " Sati mai zuwa zai kasance wuta wuta" kamar yadda ta rubuta a hoton da ta aika wa mutumin.


Yansanda sun ce Mumo zai gurfana a Kotu bisa tuhumar haddasa tashin hankali a cikin gida, haddasa matsanancin ciwo a al'aurar matarshi, tare da haddasa yiwuwar rashin haihuwa ga ,matar, daga cikin jerin laifuka da yansanda suka shirya wa Mumo.


Sai dai Lauyan Mumo ya ce, "Za mu nuna hoton tsiraicinta da matar ta aika wa wani kato, Kwarto, cewa bakin ciki da ta haddasa wa mijinta ya fi abin da mijin ya aikata mata. zamu kuma nemi Kotu ta sa a yi wa matar bulala 100, domin kaucewa tashin hankali tsakaninta da mijinta".


Mumo zai gurfana a gaban Kotu a garin Kitui ranar Litinin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN