Mata yanzu suna tafasa audugar mata suna shan ruwan don maye - NDLEA


Rahotun Legit Hausa

Hukumar kula da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) reshen jihar Gombe ta ce mata a jihar sun kirkiro da wata sabuwar hanyar yin maye. A wani taron wayar da kan jama'a a jihar, kwamandan da ke kula da yankin Funakaye na hukumar, Muhammad Alkali, ya ce matakin shaye shayen miyagun kwayoyi a tsakanin mata a Gombe ya karu ne daga jaraba ta al'ada zuwa kwayoyi zuwaga yanzu shan tacaccen ruwan tafasasshen audugar al'ada ta mata domin maye.

“An jawo hankalin mu zuwa ga cewa galibin masu shan kwayoyin sun yi wata dabara ta yin maye ba tare da shan abubuwan da doka ta hana ba ko kuma sanannun kwayoyin maye.

A yanzu suna tafasa audigar tsafta ta mata hade da wasu abubuwan, galibi shara, suna tace ruwa kafin a sha "Kun ga wannan mummunan abu ne a ga mutane, hakika al'ummarmu tana matukar bukatar taimakon dukkan masu fada a ji a cikin wannan gwagwarmaya tunda NDLEA ba zata iya ita kadai ba".

A wani rahoton, kun ji cewa a kalla mutane 13 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota da suka faru a jihar Bauchi a daren ranar Alhamis da safiyar ranar Juma'a. The Punch ta ruwaito cewa hatsarin motocin sun faru ne a Tashan Maiturare da Takandan Giwa duk a babban titin Bauchi zuwa Jos a karamar hukumar Toro a jihar ta Bauchi.

A hatsarin na farko wadda ya faru misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis, a kalla mutane 11 ne suka mutu nan take yayin da wasu da dama suka jikkata. Hatsarin na biyu ya faru ne a subahin ranar Juma'a kusa da kauyen Takandan Giwa yayinda wata mota ta kauce daga titi ta fada cikin daji inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu rauni.

Da aka tuntube shi, Shugaban sashin ayyuka na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, Ibrahim Abubakar ya tabbatar da afkuwar hadduran amma ya ce har yanzu suna tattara bayanai.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN