Rahotun Legit Hausa
Hukumar yaki da cin da rasha wa da karya tattalin arziki (EFCC) ta bankado yadda tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji, ya shafe tsawon shekaru takwas (8) yana wawurar miliyan N500 daga asusun jihar lokacin da yake kan karagar mulki. EFCC ta ce tsohon gwamnan ya fara kwasar kudin ne tun lokacin da yake rike da mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Abia a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Orji Uzor Kalu, wanda aka yanke wa hukuncin dauri bayan samunsa da laifin tafka almundahana.
Hukumar ta fara binciken hada hadar kudade da tsohon gwamnan ke yi bayan ta karbi wani korafi da wata kungiya mai rajin yaki da cin hanci, 'Save Nigeria Group', ta aika mata a kansa. A cikin takardar korafin, kungiyar ta yi zargin cewa dukkan kudaden da gwamnan ke fitar wa duk wata daga asusun jihar, suna tafiya ne wajen biyan bukatun kansa.
Kungiyar ta bayyana cewa N500m da gwamnan ke fitar wa duk wata basa daga cikin kudaden da jihar ke kashe wa a kan harkokin tsaron jihar. Wata majiya ta bayyana cewa EFCC ta fadada bincikenta zuwa kan wasu 'yan uwa na jini ga tsohon gwamnan domin bankado rawar da suka taka a cikin badakalar da ya tafka.
Majiyar ta bayyana cewa babban dan tsohon gwamnan, Chinedum, wanda yanzu haka shine shugaban majalisar dokokin jihar Abia, tare da dan uwansa sun zama sanannu fuskoki a hukumar EFCC saboda yawan gayyatarsu domin amsa tambayoyi a kan abinda dangane da badakalar kudaden. EFCC ta bankado a kalla asusu 100 da ke da nasaba da Chinedum tare da gano wasu asusu fiye da 145 na 'yan uwan tsohon gwamnan da ya yi amfani da su wajen karkatar da biliyan N150.
Daga cikin kudaden jihar da tsohon gwamnan ya dinga samun damar cire N500m kowanne wata akwai kason da jihar ke karba kowanne wata daga gwamnatin tarayya N383bn, kudin rarar man fetur N55bn, kudin Sure-P N2.3bn, kudin kiyaye kwararowar hamada N8.1bn da bashin banki N10.5bn da jihar ta karba ta hannun ma'aikatar kananan hukumomi da sauransu. Mukaddashin kakakin EFCC, Tony Orilade, ya tabbatar da cewa hukumar tana gudanar da bincike a kan badakalolin kudi da suka shafi Theodore Orji
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari