Duba hotunan abin da Gwamnatin jihar Lagos ta yi a wani kasuwa

Gwamnatin jihar Lagos ta rushe babban kasuwar gwanjo da aka fi sani da suna kasuwae Katangua. Wannan kasuwa ta shahara wajen baje kayakin da aka shigo da su daga turai da ake kira Osho,Okrika,ko Gwanjo da kalmar Hausa.

Dubannin masu sana'ar gwanjo a wasu sassa na Najeriya sun dogara ne da wannan kasuwa wajen zuwa domin su yi sarin kayaki da suke zuwa su sayar a Jihohinsu. Wannan mataki na Gwamnatin jihar Lagos, ya zo ne bayan dokar hana sufurin babur da ake kira Okada ko Achaba, da Keke Napep a fadin jihar.

A wani rahotun kuma, ranar Litinin, an sami barkewar rikici tsakanin jami'an yansanda da na yan acaba da suka nemi su gudanar da zanga zaangan nuna rashin amincewa da dokar. Amma lamari ya kazamce bayan yansanda sun yi kokarin hana su. Rahotanni sun yi zargin cewa an kashe mutum 3 a rikin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari