Jami'an rundunar yansanadan jihar Abia, sashen SARS, karkashin jagorancin babban jami'in sashen SP
Obioguru Johnbull, sun bindige wasu yan fashi da makami da satar mutane a maboyarsu da ke Ekeakpara, a karamar hukumar Osisioma.
ISYAKU.COM ya samo cewa yansandan sun kai samamen bazata ne a maboyar yan fashin, kuma yayin da harbe harbe ya kaure, wasu yan fashin sun tsere, amma yansanda sun bindige wasu daga cikinsu.
Sakamakon wannan samame, yansanda sun ceto wasu mutane da yan fashin suka sace, wadanda suka hada da Michael Maduchukwu mai shekara 39, an sace shi ranar 31/01/2020 a Ariaria kusa da magamar hanya ta St. Mary, Aba,
sai Emeka Emenyeonu mai shekara 38, wanda aka sace ranar 01/02/2020 a Asa Umudim,
Aba da kuma wata mace mai suna Mercy Akuka yar shekara 30, an sace ta ranar 01/02/2020 a Umudim
Aba.
Babu jami'in dansanda da ya sami rauni a wannan samame, kuma yansanda sun gano makamai da yan fashin ke aamfani da su.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari