Idan
aka ce Hepatitis Kai tsaye ana nufin ciwon Hanta a Hausance. Sunan
cutar ya samo asaline daga yaren Greek (Girka); “Hepato”=Liver =Hanta,
sannan “itis” dafi (prefix) ne da ya ke nufin radadi a kimiyyance
Hepatitis
(wato ciwon Hanta) Yana da Ire-ire Har Guda Biyar; Hepatitis A,
Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E. Cikinsu Akwai Masu
Bacewa da Kansu Bayan Sun Kama Mutum, Wasunsu Kuma Sai Anyi Magani. Haka
Nan Wasunsu Basa Tsananta, Wasunsu Kuma Suna Tsananta.
Sai dai Bincike Yayi Nuni da Cewa; Hepatitis A, Hepatitis B, da Kuma Hepatitis C sune Suka fi Wanzuwa Tsakanin Mutane.
Kowacce
cikinsu alamominta, abinda yake haddasata, yadda ake maganceta,
hanyoyin kamuwa da Ita, yadda ake kare afkuwarta ya banbanta da kowacce.
Kamar
Yanda Bincike Ya Nuna A Shekarar 2015 A Kalla Mutane 114 Million Ne Ke
Dauke da “Hepatitis A” a Duk Fadin Duniya, Yayin da A Kalla Mutane 343
Million Ne Ke Dauke da “Hepatitis B”, Haka Nan A Kalla Mutane 142
Million Ne Ke Dauke da “Hepatitis C” A Duk Fadin Duniya. A Kalla Mutane
Miliyan Dayane Ke Rasuwa duk Shekara A Kuma Duk Fadin Duniya Sanadiyar
Hepatitis.
A
kasar Amurka akalla mutane 250,000 ne ke kamuwa da wannan cuta a duk
shekara, yayinda akalla mutane 75 ke rasuwa a duk shekara sanadiyar Hepatitis.
ALAMOMIN CIWON HANTA
-Hepatitis A:-
Ciwon Ciki (Abdominal Pain), Zafin Jiki (Fever), Amai (Vomiting),
Tashin Zuciya (Nausea), Kasala (Fatigue), Bakin Fitsari (Choluria),
Idanuwa da Fata su koma rawaya-rawaya (Jaundice Symptoms) da sauransu.
Kwata-kwata Bata tsananta Bayan Mutum Ya Kamu da Ita.
-Hepatitis B:–
Zafin Jiki (Fever), Kasala (Fatigue), Yellow Idanuwa da Yellow Fata da
Idanuwa (Jaundice Symptoms), Gudawa (diarrhoea), da Kuma Wasu Alamomi
Masu Kama da Cutar” Flu”. Wani Lokacin Ma Bata Nuna Alama. Tana Iya
Tsananta da Kaso 10 cikin Dari Na Mutanen da Suka Kamu da Ita.
-Hepatitis C:- Iri Dayane da Hepatitis B. Sai dai wannan tana iya tsananta da Kaso 75-80 cikin Dari Na Mutanen da Suka Kamu da Ita.
TSAWON KWANAKI DAGA LOKACIN SHIGAR KWAYAR CUTAR CIKIN JIKIN MUTUM IZUWA LOKACIN BAYYANAR ALAMOMINTA (INCUBATION PERIOD)
-Hepatitis A:- Sati Biyu Zuwa Sati Bakwai (2-7 weeks). -Hepatitis B:- Sati Shida Zuwa Sati Ashirin da Uku (6-23 weeks).
–Hepatitis C:- Sati Biyu Zuwa Sati Ashirin da Biyar (2-25 weeks).
–Hepatitis C:- Sati Biyu Zuwa Sati Ashirin da Biyar (2-25 weeks).
ABUBUWAN DA SUKE HADDASATA CIWON HANTA
-Hepatitis A:- Abinda Yake Haddasata Shine Wani Kwayar Cuta da Ido Baya Iya Gani Mai Suna” Hepatitis A Virus” (HAV).
-Hepatitis B:– Hepatitis B Virus (HBV).
-Hepatitis C:- Hepatitis C Virus (HCV).
Sannan Yawan Shan Giya, Guba (toxic substances), Matsalar Garkuwar Jiki (Autoimmune diseases), Yin Amfani da Kwayoyin Magani Ba Bisa Ka’ida Ba, Gado (Genetic cause), da sauransu Na Iya Haddasa ciwon Hanta.
HANYOYIN KAMUWA DA CUTAR CIWON HANTA
-Hepatitis A:-
Gurbatuwar Abinci Ko Ruwan Sha Wanda Ya Gaurayu da Kashin Wani Mai
Dauke da Cutar, Wanda Kwaruna (Flies) Ke Yadawa, da Kuma Hada Jiki (Body
Contact) da Sauransu.
-Hepatitis B:-
Idan Aka Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Ita (Transfusion of infected
blood), Yin Amfani da Allura Ko Razor Masu Dauke da Kwayar Cutar (Use of
infected sharp objects), Daga Uwa Zuwa Danta (Mother to Newborn),
Lokacin Saduwa da Mai Dauke da Cutar (Sexual contact), da Sauransu.
-Hepatitis C:-
Sanyawa Mutum Jinin Mai Dauke da Cutar (Transfusion of infected blood),
Amfani da Allura Ko Razor Mai Dauke da Kwayar Cutar (Use of infected
sharp objects), Musayar Abubuwan Tsafta Wanda Mutum Dayane Ya Kamata
Yayi Amfani Dashi ( Sharing of personal hygiene implements), da
sauransu.
YADDA AKE GANO CUTAR A JIKIN DAN ADAM
Ana
Iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin Mutum Bayan Alamunta
Sun Fara Bayyana, Daga Nan Sai Ayi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin
Mutum.
YADDA AKE MAGANCE CUTAR HEPATITIS
Maza garzaya asibiti mafi kusa da kai/ke don saduwa da ma’aikacin lafiya da darar ka/kin fara Jin alamomin dana ambata a sama.
HADURAN DAKE TATTARE DA WANNAN CUTA
Babban
Hatsarin Dake Tattare da Wannan Cuta Shine; Hantar Mutum Zata Iya
Lalacewa ta Yanda Dole sai Dai A Chanza Masa Wata, Idan Kuma back Allaah
Ne Ya Kiyaye Ba to Mutum Na Iya Rasa Ransa.
YADDA AKE KARE JIKI DAGA AFKUWAR CUTAR
Ana
Iya Kare Afkuwar Wannan Cutane ta Hanyar Yin Allurar Rigakafi.
Hepatitis Vaccine sunan Allurar. Ita Kuma Ana Yiwa Mutum Ne da Zarar An
Haifeshi, Sai Kuma A Sati Na Shida, Sati Na Goma, da Kuma Sati Na Goma
sha Hudu da Haihuwar Jariri/Jaririya. A Dunkule Ana Kiran Alluran da
Takwarorinsu da Suna “Pentavalent Vaccine”. Sai Kuma Inganta Tsaftar
Jiki Data Muhalli, da Kuma Kiyaye Hanyoyin Kamuwa da Cutar.
Allaah Ya Kare Dukkanin Al’ummar Musulmi Daga Sharrin Wannan Cuta Amin.
Daga-Ya’u Muhammad Sani (Senior Community Health Extension Worker (SCHEW).
DAGA ISYAKU.COMLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari