• Labaran yau


  Yansanda sun kama shugaban kungiyar asiri a jihar Kudu

  Hukumar yanandan jihar Lagos ta kama  wani matashi mai suna Olowolayemo Sodiq dan shekara 23 wanda ake zargi da kasancwa jagoran yan kungiyar asiri a yankin Bariga a birnin Lagos.

  Ana zargin Sodiq ya hada baki da Bamidele Moses suka kwace babur kirar Bajaj daga hannun wani saurayi mai suna Jude Saka a watan Disamba 2019. Amma yansandan Bariga sun kama Bamidele.

  Kakakin hukumar yansandan jihar Lagos Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce " Wanda suka hada baki suka aikata laifin tare yansandan Bariga sun kama shi, kuma an mika shi ga sashen bincike na SARS domin gudanar da bincike".

  DAGA ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda sun kama shugaban kungiyar asiri a jihar Kudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama