Jami'an rundunar yansandan jihar Anambra sun yi nassarar bindige yan fashi da makami guda biyu bayan wani musanyar wuta da bindigogi. Wadanda aka kashe su ne Onyebuchi Ngala wanda aka fi sani da suna Ceaser da kuma Izuchukwu Okoro.
Kakakin hukumar yansanda na jihar Muhammed Haruna, ya ce wadanda aka kashe, sun dade suna addabar mazauna birnin Awka da kewaye. Ya ce yansanda sun bi su zuwa maboyarsu a Nkwo Agulu, kuma ganin yansanda ke da wuya sai yan fashin suka buda ma yansanda wuta ta hanyar harbi da bindigogi.
Sakamakon haka yansanda suka mayar da martani kuma suka aika yan fashin barzahu.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari