Type Here to Get Search Results !

Main event

Mulki dadi: Yadda tsohon gwamnan Imo ya fashe da kuka a ofis sakamakon kwace kujerarsa

Wani hoton karshe da aka samu kai tsaye bayan Kotun koli na Najeriya ta sanar da kwace kujerar tsohon Gwamnan jihjar Imo karkashin jam'iyar PDP  Emeka Ihedioha ya fashe da kuka yayin da yake zaune a kan kujerar mulki a ofishinsa dai dai lokacin da aka sanar da kwace kujerar daga hannunsa.

Kotun koli ta kwace kujerar daga hannun Emeka Ihediohana jam'iyar PDP ta ba Hope Uzodinma na jam'iyar APC tana mai cewa an cire kuri'u daga mazabu 388 da aka kidaya wanda aka ce bisa kididdigan ne aka mika wa Ihediaha kujerar.

Kotun ta ce kuri'u da aka dakatar da su sun kai 213,295, sakamakon haka aka ce Ihedioha ne ya ci zabe bisa kuskuren sakamakon kuri'u daga na'urar komputa.

Daga karshe Kotun ta yi umarnin cewa hukumar INEC ta karbe takardar shaidar cin zabe daga hannun Emeka Ihedioha na jam'iyara PDP ta mika sabo ga Hope Uzodinma na jam'iyar APC.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies