An yi wa ofishin jakadancin Amurka luguden rokoki a kasar Iraqi

An yi wa ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Iraqi luguden rokoki ranar Lahadi, lamari da ya yi sanadin mutuwan wasu fararen hula bayan saunkan rokokin a wani gini da ke ofishin jakadancin.

Mazauna unguwan sun ce an jiyo karar fashewar rokokin a yankin mafi tsaro na Green Zone wanda nan ne mazaunin ofishin jakadancin Amurka yake kuma mazaunin Gwamnatin Iriqi.

Wannan yana faruwa ne bayan tada zaune tsaye da ya samo asali bayan shugaban Amurka Donald Trump ya umarci mayakan sojin sama na kasarsa suka kashe wani babban Janar na sojin Iran Qassem Soleimani a cikin kasar Iraqi sakamakon harin da suka kai masa yayin da yake kan hanyar filin jirgin sama na Iraqi..
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari

LATSA NAN DOMIN ZAMA WAKILINMU A GARIN KU 
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN