An kama yan mata 32 bisa zargin yin karuwanci a jihar Kano

Jami'an hukumar Hisbah na jihar Kano sun kama mata 32 da ake zargi da aikata karuwanci. An kama yan matan ne a wani samame da jami'an hukumar suka kai a wurare da ake zargin ana aikata wannan harka bayan hukumar ta sami bayanan sirri.

Daraktan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Haruna Muhammad Sandi Ibn Sina, ya umarci jami'an hukumar su gudanar da cikakken bincike, domin ganin yadda za a tsara mataki da za a bi domin ganin yan matan sun daina wannan harka.

Ya kuma zanta da iyayen wasu daga cikin yan matan wadanda ke sanye da Hijabi da hukumar ta dinka masu, daga bisani ya yi wa matan wa'azi.

Ya kuma kara da cewa duk wacce aka sake kamawa zata fuskanci hukuncin dokokin Shari'a na jihar Kano.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post