Dokar social media: Majalisan tarayya ba za ta sa hannu a dokar batancin ba - Ahmed Lawal


Bayan dimbin koke koke tare da korafe korafe daaga dubu dubatan yan Najeriya kan dokar kalaman batanci, shugaban majalisar Dattawa na Najeriya Ahmed Lawan ya ce Majalisar Dattawa ba za ta amince ta sa hannu a dokar ba.

Lawal ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan wani koke da wata kungiya mai suna kungiyar marubuta masu kare hakkin bil'adama Human Rights Writers Association of Nigeria, HURIWA.  ta rubuta.

Shugaban majalisar Dattawan ya ce yan majalisa za su saurari koken yan Najeriya  game da waannan dokar kuma za su yi abin da yan Najeriya suke bukata.

Wannan yana kunshe ne a wata takarda da shugaban maajalisar Dattawan ya rubuta wa HURIWA ranar 20 ga watan Nuwamba 2019 kuma shugaban maa'aikatan zauren majilisan dattawa Alhaji Babagan M. Aji ya karba ranar 4 ga watan Disamba 2018 mai taken " DALILIN DA YA SA DOKAR MAJALISA KAN YANCIN FADIN RA'AYI BAYA BISA TSARIN DOKA:  DAGA HURIWA".


Abin da wasikar ta kunsa:

" Na rubuto domin in gabatar maku da gaisuwan shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawa n Phd, CON kuma in tabbatar maku da cewa mun karbi wasikarku kan  wannan zance da ke takaddama akai, inda kuka bukaci Majalisan Dattawa ta jinginar da da wannan yunkuri na dakile yancin  amfani da shafukan sada zumunta.

"Maigirma shugaban Majalisan Dattawa ya yaba wa kokarinku na ganin an yi abin da yake kunshe a kundin tsarin mulkin Najeriya, da kuma yadda manbobin ku suka yi amfani da basirarsu kasancewarsu marubuta suka kare martaba da mutuncin hakkin bil'adaman Najeriya".

"Sakamakon haka Maigirma shugaban Majalisar Dattawa yana atabbata maku cewa Majalisar Dattawa ba za ta sa hannu a dokar da jama'a  basu so ba. Yayin da yake yi maku godiya, ya bukaci ku yi amannan da tabbaci  kan matsayin da shugaban Majalisar Dattawa ya dauka kan wannan lamari".


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari

Previous Post Next Post