Isyaku Garba ba dan Shi'a bane kamar yadda yan waya suka yi masa kazafi a Birnin kebbi

Garin Birnin kebbi
Masoya Mujallar ISYAKU.COM sun bukaci mu fitar da bayani sakamakon yadda wasu mutane marasa kyakkyawar manufa a rayuwa suke zagayawa suna cewa Mawallafin ISYAKU.COM dan Shi'a ne.

Bisa wannan dalili ne ya sa muka amsa kiran dubban masoyanmu domin mu sanar da masu karatu cewa Isyaku Garba wanda shi ne Mawallafin ISYAKU.COM ba dan Shi'a bane, kuma baya da alaka da Shi'a.

Idan har Mujallar ISYAKU.COM ya buga labaran Shi'a a garin Birnin kebbi, baya nufin kasancewarsa dan Shi'a. Kamar yadda BBC Hausa, DW-Hausa, RFI Hausa, TRT Hausa da sauran Jaridu sun sha wallafa labaran Shi'a  domin labari ne kawai. ISYAKU.COM ya sha wallafa labaran Darika da sauran kungiyoyin Musulunci kuma kyauta.

Mun kalubalanci masu yi mana kazafi su je su bincika da kansu a wajen yan Shi'a.  Aikin labarai da rahoyu bai da addini, kabilanci ko bangaranci .

Wannan ya samo asali daga wasu abokan adawa wajen sana'a wadanda suka mayar da jayayya da hukuncin Allah wani abun ado. Wadannan mutane jahilci ya riga ya hudasu ta yadda babu wani alhairi a tunaninsu sai dai yadda za su cuci wannan ko yadda za a kulla ma wancan munafunci, sharri kazafi da karya. 

Daga karshe muna tabbatar wa mai karatu cewa Isyaku Garba Zuru ba dan Shi'a bane, ba matsafi bane, ba dan Luwadi ba ne, kuma yana Sallah, amma an yi masa kazafi an alakanta shi da wadannan alkaba'i daga asalin wasu rikakkun fasikai wadanda suka yi haka, bisa manufar ganin sun hana wanzuwar ayyukanmu na ci gaba a cikin garin Birnin kebbi.

Muna rokonku ku kalubalanci duk wanda ya zo maku da wani batanci game da mu domin ya baku hujja akan kazafi da yake yi wa Isyaku Garba, nan take za ka gane cewa kabilanci da hassada ne kawai, Allah shi ne madogaran mu, kuma shi zai iya mana, domin an yi wa Annabawa balle mu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post