Zaben Kogi: Dan takaran PDP Musa Wada ya ce bai amince da sakamako ba

Legit Hausa
Tun kafin sanar da dukkan sakamakon kananan hukumomin da ke jihar Kogi da aka yi zabe a jiya Asabar, dan takarar jam'iyyar PDP, Musa Wada ya ce bai aminta da sakamakon ba.
A yayin zantawa da manema labarai a garin Lokoja a ranar Lahadi, wanda a lokacin ne ake sanar da sakamakon zaben na kananan hukumomi 21 na jihar, Wada ya zargi cewa sakamakon duk na bogi ne.
Ya ce, abinda ya faru a jihar a cikin ranakun karshen makon ya yi karantsaye ga damokaradiyya da kuma burin mutanen jihar Kogi.
Ya ce, abinda ya faru yayin zaben bai bayyana gaskiyar ra'ayin mutane jihar ba.
Ya kara da jajanta yadda jami'an tsaro suka hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta don dakile ra'ayin mutanen jihar Kogin.
Ya ce babu bukatar zabe, "Idan har Okene da ke da tantattun masu kada kuri'a dubu arba'in zasu kawo kuri'u dubu dari da sha biyu." Ya ce wannan mummunar rana ce ga mutanen jihar Kogi don kuwa suna ta makoki.
"Wa kuka ga yana murna? Haka take kasancewa bayan nasara? Ba don ni bane, don mutanen jihar kogi ne da ke cikin mummunan hali na shekaru hudu," ya ce.
"Na lashe zaben da aka yi cikin gaskiya. Kalli yadda suka bar guraren da aka yi magudi kamarsu Okene. Akwai wurare da yawa da aka kwace akwatunan zabe. Da anyi abinda ya dace, ba shakka ni zan lashe zaben," ya bayyana.
Kamar yadda yace, jam'iyyar APC ta maida Najeriya halin da ta ke ciki a da.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post