Yanzu-yanzu: Babu wanda yafi Buhari iko a mulkinsa - Garba Shehu ya tabbatar da koran hadiman Osinbajo

Legit Hausa
Bayan kwana biyu ana rade-radin cewa shugaba Muhammadu Buhari dake Landan ya sallami wasu hadiman mataimakinsa, Yemi Osinbajo, akalla guda 35 ba tare da wani laifi ba, mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya fito ya raba gardama.
Garba Shehu ya bayyana cewa ba wani abu bane don shugaban kasa ya rage hadiman mataimakinsa a duk lokacin da ya ga dama kuma ba shi bane farau ba.
Garba Shehu yace: "Fadar shugaban kasa na son tabbatarwa al'umma cewa akwai sauye-sauye da ake yi cikin gwamnatin nan, musamman rage nade-nade da sallamar wadanda aka nada a wa'adi na biyu."
"Shugaba Buhari ne ya bada umurnin yin hakan domn rage yawan ma'aikata. Hakazalika wannan martani ne ga wadanda suke cewa ma'aikata sun yi yawa a fadar shugaban kasa."
"Ofishin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta bi umurnin shugaban kasa, kuma ta rage yawan ma'aikatanta."
"Babban dalilin da yasa aka yi haka shine tattalin kudin al'umma da gabatar da ayyukan da jama'a ke bukata."
"Tun da aka fara mulkin nan, yawan hadiman shugaban kasa bai kai na mataimakin shugaban kasa ba kuma an dade ana son rage yawan ma'aikatan fadar shugaban kasa."
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post