Yansanda sun kama dansandan MOPOL da ya karbi cin hancin N15.000, karanta dalili

Hukumar yansanda ta gano tare da kama wani jami'in dansanda da aka gani a wani faifen bidiyo yana karbar cin hanci na N15.000 daga hannun wani mai mota a birnin Lagos.

Hukumar yansanda ta wallafa sanarwar a shafinta na Twitter cewa ta cafke karamin dansanda da aka gani a wannan faifen bidiyo mai suna Sgt. Onuh Makedomu mai lambar aikin dansanda 431625 wanda ke aiki da sashen yansandan kwantar da tarzoma 49 MPF, amma yake aiki na musamman a sashen sintiri a manyan hanyoyi na Lagos.

Sanarwar ta kara da cewa Safeto Janar na yansandan Najeriya ya yaba wa mutumin da ya yi karfin hali da jarunta wajen dauko hoton bidiyon wannan batagarin dansanda, cewa ya je wajen Kakakin hukumar yansanda na jihar Lagos domin ya karbi kudinsa da dansandan ya karba a wajensa.

Sgt.  Onuh na fuskantar Kotun cikin gida na hukumar yansanda da ake kira Orderly room, bisa tuhumar zubar da mutuncin aikin dansanda da kwace.DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post