Karanta abin da Sarki Bayero ya yi wa shugabannin Ibo game da satar yaran Kano

Legit Hausa

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero ya tashi daga kasar
Kano zuwa Kudu maso Gabashin Najeriya a game da matsalar satar kananan
yaran da ake fama da ita a jihar Kano.

Kamar yadda mu ka samu labari,Sarkin ya fara wannan ziyara ne tun Ranar Alhamis, 7 ga Watan Nuwamba,inda ya ziyarci gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, da kuma jami'an
tsaro. Daga nan Mai martaban ya zarce jihar Imo, ya samu zantawa da
Emeka Ihedioha.

Wannan ziyarar sabon Sarkin ta kai sa har gaban
Dattawan na kasar Ibo irinsu Cif Emmanuel Iwuanyanwu. Emmanuel
Iwuanyanwu ya karbi bakuncin Sarkin na Bichi da Tawagarsa ne a gidansa
da ke babban birnin jihar Imo na Owerri a Ranar Lahadi kamar yadda
Jaridar The Nation ta rahoto Iwuanyanwu ya yi wa Sarkin karin haske
kan kokarin da ake yi na nunawa Duniya mutanen Ibo ba su son shugaban
kasa Muhammadu Buhari,

Cif Iwuanyanwu ya ce hakan ba gaskiya ba ne. A cewar Iwuanyanwu, abin da mutanen kasar Kudu maso Gabashin Najeriyar su ke so shi ne a rika yi wa kowa adalci a kasar. Dattijon ya yabawa
shugaban kasa Muhamadu Buhari a zaman The Nation ta rahoto Dattijon na
kasar Ibo ya na yabon halin shugaban kasa Buhari na gaskiya da rikon
amana. Emmanuel Iwuanyanwu ya ce Buhari mutum ne da bai da kashin
rashin gaskiya.

Satar yaran da ake yi a Arewa ya zama ruwan dare, don
haka Sarki Aminu Ado Bayero ya nemi ya zauna da mutanen Kudu maso
Gabashin kasar da nufin ganin an daina wannan danyen aiki.
Previous Post Next Post