• Labaran yau

  Mahaifina da kanshi yake duba budurcina ya tabbatar da babu matsala - Jaruma Halima Abubakar

  Legit Hausa
  Fitacciyar 'yar wasan kwaikwayon nan ta masana'antar fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood, Halima Abubakar ta bayyana ra'ayinta akan maganar da fitaccen mawakin nan na kasar Amurka, T. I yayi, inda ya bayyana cewa duk shekara yana kai 'yarsa asibiti don likitoci su tabbatar masa cewa babu matsala tattare da budurcinta.
  Fitacciyar jarumar Halima Abubakar ta bayyana cewa ita ma mahaifinta yana kaita asibiti don duba budurcinta a lokacin da ta fara girma. Ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a ranar Alhamis dinnan da ta gabata, 7 ga watan Nuwambar shekarar 2019.
  Jarumar ta yi tsokacin ne yayin mayar da martani ga fitaccen mawakin T. I akan duba budurcin 'yarsa da yake yi akai-akai. Kamar yadda jarumar tace, babu wani aibu idan mahaifi ya kai 'yarsa don duba budurcinta.
  A wannan lokaci da muke ciki dai iyaye na ta faman kaffa-kaffa da 'ya'yansu musamman ma mata wadanda suke iya daukar ciki da zarar sun sadu da saurayi, hakan ne ya sanya mahaifin jarumar kai ta asibiti domin tabbatar da cewa babu wata matsala tattare da 'yar tasa.
  DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mahaifina da kanshi yake duba budurcina ya tabbatar da babu matsala - Jaruma Halima Abubakar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama