An kama wani dansanda da ke sayer wa Boko Haran kwayar Tramal

Rundunar hana sha da tu'ammali da miyagun kwayoyi NDLEA na jihar Yobe, ta kama wani jami'm dansanda da ke safara tare da sayar wa kungiyar Biko Haran kwayar Tramal mai nauyin kg59 a garin Gwoza na jihjar Borno.

Kwamandan rundunar na jihar Yobe Mr. Reuben Apah ne ya shaida wa manema labarai haka a Damaturu babban birnin jihar Yobe ranar 7 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa dansanda da aka kama, ya ce, ya sayo kwayoyin ne daga wajen wani jami'in hukumar hana fasa kwabri NCS a jihar Lagos.
 
DAGA .ISYAKUCOM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post