Duba wani al'adar Dakarkari na kasar Zuru da zai baka mamaki | ISYAKU.COM


Al'umman Dakarkari mutane ne masu alfahari da al'adunsu na gargajiya wanda ya hada da rawan gargajiya, farauta, noma da kiwo. C'lela a Dakkarce, asalin dan Zuru kenan mai asalin suna Azugru kafin Turawan mulkin mallaka su mayar da shi Zuru.

Dakkarawa na kudancin jihar Kebbi, wanda ke da al'adar aiki tukuru kuma da gaskiya a duk inda suka sami kansu. Hakazalika an shaidi matansu da biyayan aure a duk yanayi da suka sami kansu, ga hakuri da rufa wa miji asiri a lokacin da ya sami kanshi cikin wani kuncin rayuwa.

Masarautar Zuru na da kananan hukumomi da suka hada da Zuru, Sakaba, Fakai da Danko -Wasagu.

An kiyasta cewa Musulmi na da adadin kashi 50, Kiristoci na da kaso 40, yayin da yan gargajiya na da kaso 10 a yawan jama'ar kasar Zuru.

Masarautar Zuru na da Sarki mai Sanda, wanda ke shugabanci da tsarin Mulkin Daulan Usmaniyya, duk da yake tarihi ya nuna cewa ba'a ci kasar Zuru da yaki lokacin Jihadi ba. Sakamakon haka ya sa al'umman kasar Zuru suka karbi Musulunci don rabin kansu.

Kalli daya daga cikin rawan gargajiya na Dakarkari:DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post