Likita ya ceto ran dattijo a jirgin sama ta hanyar tsotse fitsari daga mararsa (Bidiyo)

Legit Hausa
Matafiya sun shiga jirgin China Southern Airlines kamar yadda aka saba daga Guangzhou zuwa New York a kasar Amurka.
Sai dai a wannan ranar an samu afkuwar rashin lafiya na gaggawa yayin da wani dattijo ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali.
Dattijon ya kasa yin fitsari da kansa duk da cewa mafitsararsa ta cika da fitsari kimanin 800ml.
TimesLIVE ta ruwaito cewa daya daga cikin fasinjojin da ke jirgin mai zuna Zhang Hong, wadda likita ne mai tiyata ya yi jarumta ya kaiwa dattijon dauki.
Ya yi amfani da allurar sirinji, abin tsotso ababen sha wato 'straw' da kuma na'urar shakar iskar oxygen nan take ya fara zuko fitsari daga marar dattijon kuma ya cigaba da hakan har na tsawon mintuna 37.
Ga bidiyon likitan yayin da ya ke tsotso fitsari daga marar dattijon yana zubarwa cikin wani kwalba.
https://www.youtube.com/watch?v=W8iAJ4blu-0
A cewar The South China Morning Post, akwai yiwuwar dattijon zai iya rasa ransa da Hong bai taimaka masa ba.
Legit.ng ta gano cewa likitan ya yi wannan aikin na gaggawa ne yayin da jirgin ke da ta tafiyar awanni shida a gabansa kafin su isa inda za su sauka.
Hong ya ce: "Da na lura cewa mutumin ba zai iya jure ciwon ba, abinda na ke tunani kawai shine yadda zan fitar da fitsarin da ke mararsa."
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN