Yan fashi sun kai hari wani banki a Ekiti, sun kashe dan sanda suka tsere da kudadeLegit Hausa

An tattaro cewa fashin ya afku ne da misalin karfe 2:30 na rana inda suke ta harbi yayinda tawagarsu na mutum 10 suka shiga cikin bankin na zamani. Jaridar premium Times ta ruwaito inda idanun shaida kecewa yan fashin sun kwashe akalla mintuna 25 suna fashi bayan sun shigo garin cikin motoci biyu ta hanyar Ikere.

Kakakin yan sandan jihar Ekiti, Mista Caleb Ikechukwu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace yan ta’addan sun fasa kofar tsaro na bankin da nakiya sannan suka samu damar shiga ciki. Yace jami’an rundunar na kan bin sahun yan ta’addan sannan yayi kira ga mazauna jihar da kada su sanya tsoro a zukatansu.

A wani lamarin kuma, mun ji cewa rundunar 'yan sanda reshen jihar Taraba ta ce ta kashe wani gawurtaccen dan fashi da makami da ta dade tana nema ruwa a jallo.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar na jihar Taraba, David Misal ya fitar, ya ce an yi nasarar kashe dan fashin ne bayan an sanar da 'yan sanda cewa wasu 'yan bindiga sun tare hanyar Jatau/Borno kuru-Ku a karamar hukumar Bali na jihar Taraba suna yi wa mutane fashi.

A cewar sanarwar, 'yan sandan tare da hadin gwiwa 'yan kungiyar sa kai sun garzaya inda lamarin ke faruwa kamar yadda Channels TV ta ruwaito. 
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post