Tsohuwa ‘yar shekara 87 ta kashe jikanta bisa tunanin babu wanda zai kula dashi bayan ranta


Legit Hausa

Kamar yadda jaridar ABC ta ruwaito, wata tsohuwa mai shekaru 87 a duniya mai suna Lilian Parks ta bayyana dalilin da ya sanya ta kasha jikanta saboda tana ganin cefa babu wanda zai kula mata dashi bayan ranta.

A yadda rahoton ya bayyana, Joel, marigayin yana zuwa ya zauna da kakar tashi kowanne karshe sati, sannan a ranekun aiki kuma sai yaje zauna da delibai ‘yan uwanshi. An gano gawarshi ne bayan ‘yar uwarshi taje ta duba shi a gidan kakarsu radar Lahadi dinnan da ta gabata.

Jami’an hukumar ‘Yan sanda na Bradenton sun kama tsohuwar inda suka wuce da ita domin yin gwaji a kwakwalwarta da kuma duba lafiyarta kafin a kaita kotu a yanke mata hukuncin kisa. Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce: “Wannan al’amari ne babba ga jami’an mu.

Banu ji dadi ba kwata-kwata ace mutum yana tunanin daukar ran wani saboda yana ganin ceza idan babu shi ba zam somu kulawar da ta kamata ba.” A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Bradenton din, mahaifin Joel ya rasu, mahaifiyar shi kuma tabi nesa da su.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post