Yadda wani magidanci ya kashe surukarsa da kanwar matarsa da jaririn taLegit Hausa

Ya kashe su ne a ranar 10 ga watan Satumba a garin Iguadolor a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabashin Jihar Edo kuma an gano gawarwakin wadanda ya kashe wato Mrs Alice Omorogbe 52, Mrs Blessinf Efe 25 da jaririn ta.

Edoghogho ya ce ya fusata ne ya kashe surukan nasa saboda duk lokacin da ya samu matsala da matarsa su kan dauki hayar matasa domin su lakada masa dukan tsiya. "Ni direban tifa ne amma tunda damina ya kama na koma aikin kwadago.

 "Na kashe su ne saboda fushi da nayi domin suruka ta ta kan dauki hayan matasa suyi min duka. Ta kan ce ina yi wa mata ta magana. Idan na samu rashin jituwa da mata ta, za ta aiko matasa suyi min duka. "Ban san cewa adan zai taba jaririn ba. Na tsere bayan da na kashe su.

Daga baya na dawo na fadawa mahaifi na abinda na aikata. Ban ga mata ta ba tun bayan da na kashe mahaifiyarta da 'yar uwanta." Kwamishinan 'yan sandan jihar, Danmallam Abubabakar ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike. 


DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari