Wata mata ta yiwa kanta saki uku ta hanyar tura sakon sakin ta wayar mijinta


Legit Hausa

A Musulunce mace na fita daga gidan mijinta ne idan mijinta ya furta da bakin shi cewa ya sake ta. Idan mace na so mijinta ya sake ta sai ta bi wata hanya wacce addinin musulunci ya shar'anta, inda matar za ta je gaban alkali ta nemi mijinta ya sake ta.

Zama da miji marar hakuri ga mace ba abu bane mai sauki, hakan ya saka wata Balarabiya wacce ta kasa zuwa ta nemi kotu ta raba aurensu ta bi wata hanya daban domin kawo karshen auren na su.

Matar ta shafe shekara uku tana zaune da mutumin wanda kwata-kwata ba ta kaunar zama dashi, amma kuma mutumin yaki ya bata takardarta ta saki. Hakan yasa matar ta yi kokarin yanke hukunci da kanta. Matar ta dauki wayar mijinta a lokacin da yake yin bacci ta tura sakon saki har sau uku zuwa cikin wayarta. Bayan wannan lamari ya faru, wani babban malamin addinin musulunci ya bayyana cewa wannan saki ya yiwu.

Hakan ya sa mata da mijin suka tafi kotu domin neman ta yanke hukunci. Bayan kotu ta saurari kowanne bangare, sai ta bukaci mijin ya saki matarr, amma ina maimakon ya sake ta sai ya saka shari'ar ta yi tsawo da yawa, an bayyana cewa mutumin yana yin hakan ne domin kaskantar da matar tashi a idon duniya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post