Sanya Alqur'ani cikin najasa: Gwamnan Zamfara ya sa ladan N2m ga duk wanda ya zo da bayani


Legit Hausa

Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wani bincike akan sha’anin da ke tattare da al’amarin tsintar wasu fallayen Qur’ani a najasa a makarantar Firamare a ranar Juma’a. An gano shafukan littafin mai tsarki ne a makarantar Firamare na Shattima, Gusau, wanda yayi sanadiyar rufe makarantar har sai baba-ya-gani da kuma dakatar da malaman makarantar bisa ga umurnin gwamnan jihar, Alhaji Bello Matawalle.

Gwamnan wanda a yanzu haka ya halarci taron zuba jari na Afrika a kasar Amurka, ya umurci hukumar makarantar Firamare da ya kafa kwamitin bincike akan lamarin. A wani jawabi daga babban sakataren gwamnati Alhaji Bala Maru, a Gusau a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, gwamnatin ta sanar da kafa kwamitin mutum 23, karkashin jagorancin Farfesa Jafaru Makau.

Sauna mambobin kwamitin sune manyan malaman addinin Musulunci, wakilan hukumomin tsaro, ma’aikatu da abun ya shafa, cki harda kungiyar lauyoyin Najeriya. Gwamnatin tayi alkawain bayar da kyautar naira miliyan 2 ga duk mutumin da ya kawo bayanai masu amfani. Ya bukaci jama’a musamman a Gusau da su kai rahoton duk wani motsi da basu aminta dashi ba a kewayen su zuwa ga hukumar tsaro akan lokaci.
 

Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wani bincike akan sha’anin da ke tattare da al’amarin tsintar wasu fallayen Qur’ani a najasa a makarantar Firamare a ranar Juma’a. An gano shafukan littafin mai tsarki ne a makarantar Firamare na Shattima, Gusau, wanda yayi sanadiyar rufe makarantar har sai baba-ya-gani da kuma dakatar da malaman makarantar bisa ga umurnin gwamnan jihar, Alhaji Bello Matawalle. Gwamnan wanda a yanzu haka ya halarci taron zuba jari na Afrika a kasar Amurka, ya umurci hukumar makarantar Firamare da ya kafa kwamitin bincike akan lamarin. A wani jawabi daga babban sakataren gwamnati Alhaji Bala Maru, a Gusau a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, gwamnatin ta sanar da kafa kwamitin mutum 23, karkashin jagorancin Farfesa Jafaru Makau. Sauna mambobin kwamitin sune manyan malaman addinin Musulunci, wakilan hukumomin tsaro, ma’aikatu da abun ya shafa, cki harda kungiyar lauyoyin Najeriya. Gwamnatin tayi alkawain bayar da kyautar naira miliyan 2 ga duk mutumin da ya kawo bayanai masu amfani. Ya bukaci jama’a musamman a Gusau da su kai rahoton duk wani motsi da basu aminta dashi ba a kewayen su zuwa ga hukumar tsaro akan lokaci. Read more: https://hausa.legit.ng/1262056-gwamnatin-zamfara-ta-sa-ayi-bincike-akan-batun-sanya-qurani-a-najasa-tayi-alkawarin-bayar-da-naira-miliyan-2-ga-duk-wanda-ya-kawo-bayanai.html
DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post