Yadda aka yi ma wasu yan fashi 3 bayan dubu ta cika (Hotuna)

Wasu matasa guda uku da ake zargin yan fashi ne sun gamu da fushin matasa a garin Ushongo na jihar Benue bayan sun yi ma wasu fasinjan mota fashi a yankin da safiyar yau.

Wadanda aka azabtar sun hada da Terkaa Jabi, wanda aka fi sani da suna Gajere, Terkimbir Iorbunde Ahungwaor da Paul Mbailuior Damsa.

Isyaku.com ya samo cewa wadannan matasa sun biyo wata mota ce da ta fito daga jihar Cross Rivers kuma suka kai ma fasinjojin motar farmaki, suka yi masu fashi a kusa da gidan basaraken garin Mbayegh, Chief Nathaniel Hoyo.

Hakazalika isyaku.com ya tattaro cewa basaraken ya sa wasu matasa suka bi yan fashin da suka tsere suka hau wani tsauni da ke kusa kuma suka boye a cikin kogo. Daga bisani kuma basaraken ya kira yansandan kwantar da tarzoma suka zo tare da samarin garin aka bazama cikin daji da tsaunin da ke gefen gari inda aka kama uku daga cikin yan fashin kuma aka yi ta yi masu ruwan duwatsu har suka mutu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp Latsa nan ka shiga group 7
Previous Post Next Post