Legit Hausa
An shiga halin zaman dari-dari a masarautar Gwalli a karamar
hukumar Gunmi da ke jihar Zamfara sakamakon nuna yatsa da aka fara yi a
tsakanin kabilun Hausawa da Fulani da ke zaune a yankin, kamar yadda jaridar
Daily Trust ta rawaito ranar Lahadi.
Wata majiya da ke da masaniya a kan abinda ke faruwa ta
sanar da jaridar cewa an fara samun rashin jituwa a tsakanin Hausawa mazauna
Gwalli da wasu Fulani makiyaya da suka yi hijira zuwa yankin daga karamar
hukumar Shinkafi ko Birnin Magaji a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar
Abdulaziz Yari.
"Gwamnatin baya ta umarci makiyayan da su bar yankin
bayan rigingimu tsakanin makiyaya da manoma sun yi tsanani a jihar Zamfara.
"Gwamnatin Abdulazizi Yari ta rubuta takarda zuwa masarautar Gunmi da
karamar hukuma da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro tana mai umartar
a tashi makiyayan daga yankin, bisa zargin cewa zasu iya kasancewa daga cikin
batagari.
"Bayan makiyayan sun yi hijira zuwa yankin, sai suka
fara sayen kadarori, musamman gonaki da filaye, ta hannun masu unguwa. Bayan
sun fara aiki a gonaki da filayen da suka saya ne sai sako ya zo daga sama a
kan su bar yankin.
"Wasu batagari
daga cikin mazauna yankin sai suka fake da umarnin da gwamnati ta bayar a kan
makiyayan, suka fara mayar da kadarorin makiyayan mallakarsu bayan makiyayan
sun yi hijira zuwa jihar Kebbi," a cewar majiyar. Majiyar ta bayyana cewa
dawowar da makiyayan suka fara yi yankin ne yasa jama'ar da suka mallake musu
kadarori suka shiga halin damuwa da fargaba saboda sun san cewa sun dawo ne domin
daukan fansa.
Sai dai, yanzu haka gwamnatin jihar Zamfara a karkashin
sabon gwamna, Bello Matawalle, ta gaggauta shiga tsakani tare da fara yin sulhu
a tsakanin makiyayan da Hausawa don ganin cewa ba a kara samun barkewar wani
rikici a jihar ba.
Wani mazaunin yankin mai suna Hassan Idris ya ce jami'an
'yan sanda sun gaggauta shiga lamarin kuma al'amura sun koma daidai don yanzu
haka mutanen da suka gudu sakamakon zuwan makiyayan, sun dawo gari.
Shi ma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad
Shehu, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo, ya jagoranci jami'an
tsaro zuwa fadar sarkin Gunmi, Alhaji Hassan Lawal, domin dora wa a kan zaman
sulhu da gwamnatin jihar ke yi da 'yan bindiga da sauran masu tayar da kayar
baya.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN