Mutane 70,000 sun rasa muhalli sakamakon gwabza fada tsakanin ISIS da Askarawan Nijar (Bidiyo)

Fiye da mutum 70,000 ne suka rasa matsuguni sakamakon fada da ake gwabzawa tsakanin mayakan ISIS da Askarawan kasar jamhuriyar Nijar.

Kauyen Inates da ke cikin yankin Tillaberi ya zama kango bayan jama'a sun tsere sakamakon gwabzawan fada tsakanin sassan guda biyu.

Sakamakon wannan fada da ake ci gaba da yi, tare da nakiyoyi da ke binne a kasa a wannan yankin, yana da matukar daure kai ko jama'a za su iya komawa wannan yanki nan ba da jimawa ba.

Kalli rahotun Aljazeera:

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post