Hukumar ‘yan sanda za ta kori jami’ai biyu saboda kama wa Wadume aiki

Legit Hausa
Hukumar ‘yan sandan Najeriya na daf da korar jami’anta guda biyu a dalilin zarginsu da akeyi da yin aiki tare da gawuratccen mai garkuwa da mutanen nan Hamisu Bala Wadume.
Wata majiya mai karfi daga bangaren ‘yan sandan ta shaidawa jaridar The Guardian cewa ASP Aondonna Iorbee da Sufeto Aliyu wadanda ke aiki da ofishin ‘yan sandan Ibi na daf da rasa aikinsu na ‘yan sanda.
A makon da ya gabata ne ‘yan sanda suka sake kama Wadume a Layin Mai Allo dake unguwar Hotoro ta Jihar Kano, bayan ya kubuta daga kamen farkon da aka yi masa ranar 6 ga watan Agusta a Jihar Taraba.
Wadume ya tsira ne a sakamakon wani rikici da ya kaure tsakanin ‘yan sanda da kuma sojoji a kan hanyar Ibi-Jalingo. Ya yi ikirarin cewa dakarun sojin ne suka taimaka masa ya samu kubuta.
“A kan hanyarmu sojoji ne suka biyomu suka budewa motar da muke ciki wuta, a sanadiyar haka har wasu ‘yan sanda suka mutu.
“Nan take sojojin suka tsiratar da ni inda suka sanya ni cikin wata mota mai launi ja kana muka bar nan wurin ba tare da bata lokaci ba.” A cewarsa.
Jami’an ‘yan sanda uku ne suka mutu da farar hula daya yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka saboda harbin bindiga.
Ya cigaba da cewa: “Dakarun sojin sun kai ni wurin Kyaftin Balarabe wanda ya kira DPO na ofishin ‘yan sandan Ibi domin ya bashi mabudin ankwar dake hannuna.”
“Da kansa yazo gidan ya ce bai ga mabudin ba, sai aka nemo wukar yanka karfe aka yanke ankwar nan take.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post