Zaben 2023: Dole APC sai ta shiryawa rayuwa bayan Buhari – Wani gogaggen dan siyasa

Legit Hausa

Prince Tonye Princewill wanda dan kasuwa ne, dan siyasa kuma mai shirya fina-finai shi ne yayi wannan furucin a kan zaben shekarar 2023. Prince shi ne ya rike mukamin Daraktan sadarwa na APC a jihar Rivers lokacin zaben 2019.
Haka zalika, yayi takarar gwamnan jihar Rivers a jam’iyu daban-daban ciki hadda jam’iyyar AC a shekarar 2007 da jam’iyyar Labour Party LP a shekarar 2015 kafin ya dawo cikin majar APC a shekarar 2017.
A wata hira da jaridar Vanguard tayi da shi, ya yi magana a kan mulkin Rivers da kuma yadda aka yi jam’iyyar APC tayi rashin nasara a zaben gwamnan jihar. Kana kuma ya sake fadin cewa idan har APC na son cigaba da mulki dole sai ta yi shiri domin rayuwa bayan Shugaba Buhari.
Wane irin kokarin jam’iyarku ke yi domin dinke barakar da ta auku tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Rivers lokacin zaben 2019?
Princewill: Ina mai tabbatar muku da cewa wannan barakar ta fi karfin a maganceta a matakin jiha, dole sai hedikwatar jam’iyya ta kasa ta shigo ciki. Ko shakka babu shuwagabannin APC a matakin kasa na iya bakin kokarinsu a kan wannan al’amari.
An riga da an nada ministoci yanzu, wane albishir zaku yiwa ‘yan Najeriya dangane da sabbin nadin da akayi?
Princewill: Wannan ba hurumina bane, Shugaban kasa ya riga ya fitar da tsare-tsarensa. Amma dai abinda na sani shi ne ko shakka babu da zafi-zafi za a soma gudanar da ayyuka a wannan karon.
Mutane da dama musamman ‘yan adawa na ganin cewa jam’iyyarku za ta watse da zarar Buhari ya kammala wa’adinsa a shekarar 2023, me zaka iya cewa game da wannan batun?
Princewill: Akwai wani tsohon Firai ministan Burtaniya da ke cewa “Mako guda lokaci ne mai tsawo a siyasa”. Wannan maganar ta sa zata yi amfani a nan, abinda kawai zan ce shi ne akwai bukatar shiri na musamman domin tukarar zabe mai zuwa. Ko shakka babu nasan rayuwa bayan Buhari za ta yiwa APC matukar wahala saboda Buhari da kansa ya lashe zabe ba ma sau daya ba. Amma idan kuma Buhari ya daga hannu wani a zaben mai zuwa kaga wannan mutumin zai iya karawa da ‘yan adawa.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post