Zargin N40m daga Gwamnatin jihar Kebbi, wasu masu sayar da waya sun turje wa Aliyu Tunga

Masu sayar da wayar salula tare da wasu masu gyaran wayar salula bangaren kasuwar waya na Haliru Abdu da ke garin birnin kebbi sun gudanar da turjiya a bakin shagon Aliyu Tunga da ke Olumbo Plaza kan titin Ahmadu Bello da misalin karfe 7:20 na yamma ranar Laraba saboda basu sami kudi daga cikin N40m da ake zargin cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta ba masu sayarwa da kuma gyaran waya ta hannun kungiyar HADTECH ba.

Ana zargin cewa fiye da mutum 80 ne ke harkar sayarwa tare da gyaran waya a kasuwar waya na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi, amma rahotanni sun ce ana zargin mutum 3 daga cikin adadin ne kadai suka sami wani kaso daga cikin kudaden.

Yanzu haka dai wannan lamari na zargin rashin adalci wajen rabon kudin ya haifar da rarraba tare da tsami tsakanin shugabancin kungiyar da sauran jama'a wanda ke yi ma shugabancin kungiyar kallon wofi.

Ku kasance tare da mu domin karin cikakken bayanin sakamakon bincike kan lamarin....

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN